Manchester United za ta kalubalanci dukkan kofunan bana - Onana
Asalin hoton, Getty Images
Sa'o'i 7 da suka wuce
Andre Onana ya ce Manchester United tana ta shirye-shiryen tunkarar kakar 2024/25, kuma Erik ten Hag zai kalubalanci dukkan kofunan bana.
United ta yi nasara a wasan atisayen tunkakar kakar da za a fara cikin Agusta da doke Rangers 2-0 ranar Asabar a Amurka.
Onana shi ne ya tsare ragar United a ranar, wanda shi kaɗai ne ya yi minti 90, bayan da Ten Hag ke gwada ƴan ƙwallon da zai yi amfani da su a kakar da za a shiga.
''Na yi murna da na buga wasan, domin a bara a Amurka na fara yi wa United tamaula, '' kamar yadda Onana ya ce.
''Za mu kalubalanci duk wani kofi a kakar da za a fara, mun kwan da sanin irin matsin da za mu fuskanta, amma mun yi abin kirki a kakar da ta wuce da lashe FA Cup.''
Onana ya karbi ƙyallen ƙyafti a wasan na sada zumunta a Edinburg, bayan da aka sauya Casemiro a karawa da United ta doke Rangers.
Tun kan nan United ta yi rashin nasara a hannun Rosenborg 1-0 ranar Litinin 15 ga watan Yuli, kwana ɗaya tsakani da kammala Euro 2024 a Jamus.
Ƙungiyar Old Trafford za ta fafata da Arsenal a SoFi ranar Asabar 27 ga watan Yuli daga nan ta je San Diego.
Filin wasa na Snapdragon ne zai karɓi wasan sada zumunta tsakanin United da Real Betis, wadda karawa ce da za ta kayatar.
United za ta karkare wasannin sada zumunta da fuskantar Liverpool a Carolina ranar 3 ga watan Agusta, wadda take da sabon koci, Arne Slot.
Erik ten Hag zai fara fuskantar kakar bana da Community Shield tsakanin Manchester United da Manchester City.
United ta samu wannan damar, bayan da ta ci City ta lashe FA Cup, inda ake buɗe labulen gasar tamaula ta Ingila da wasa tsakanin mai Premier da mai rike da FA Cup.
FA Cup da United ta ɗauka ya sa za ta kara a Europa League a kakar da za mu shiga, sannan za ta kece raini a Premier League da League Cup a 2024/25.